Kamfanin Dangote Ya Tsayar Da Aikinsa

0
1172

Rabo Haladu Daga Kaduna

SABON kamfanin sarrafa tumatir na Dangote ya dakatar da ayyukansa
sakamakon rashin samun danyen tumatur daga gona.
Mafi yawan gonakin tumatur da ke jihohin Kano da Jigawa da Filato da Katsina da kuma
Kaduna sun hadu da annobar wasu kwari, wanda hakan ya yi sanadin kashe dukkan
tumatirin da ke gonakin.
Wannan al\’amari ya jawo wa manoma mummunar asara, da karancin tumatir da
kuma tsananin tsadar dan ragowar tumatir din da ya saura a hannun manoman.
A farkon wannan shekarar ne kamfanin tumatir na Dangote da ke garin Kadawa a jihar Kano ya fara aiki
Inda manoma keta nona farincikinsu dangane da samun wannan kamfani a tsakiyar jihohi masu noma  tumaturi.
Tumaturi dai yanzu  yazama gol saboda yanzu  anasayar da  kwando daya akan naira dubu talatin da biyar\’wanda wata biyu da suka wuce ana sayar da kwando a kan Naira  dari uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here