Taron Fansho Domin Fadakarwa Ga Ma\’aikata Ya Yi Armashi A Kaduna

0
1125

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

Taron wayar da kawunan ma\’aikata da aka yi wa manyan masu gudanar da harkokin gwamnati ya yi armashi a Kaduna.

Taron dai an shirya shi ne domin a wayar wa da dimbin ma\’aikatan Jihar Kaduna kaikai a game da harkokin fansho  an yi shi ne a dakin taro na kula da harkokin mata a Kaduna.

Kamfanonin fansho sun bayyana irin amfanin da ke tartare da batun fansho musamman idan ma\’aikaci ya bar aiki.

Da yake bude taron gwamnan Jihar Kaduna Wanda sakataren gwamnati Lawal Balarabe Abbas, ya CE babu ko shakka batun fanshon da ma\’aikaci zai rika Tarawa kafin ya bar aiki itace mafita don haka gwamnatin Jihar Kaduna za ta ci gaba da taimakawa shirin domin ma\’aikata su amfana.

Ya kuma CE irin wannan shirin zai magance matalolin fanshon da ake fama da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here