ANA ZARGIN WATA MATA AMINA DA AUREN MAZAJE BIYU

0
1848

DAGA USMAN NASIDI

WATA kotun yanki a garin Jibiya da ke Jahar Katsina tana sauraren wata kara da ake zargin wata mata da bata wa wata matar aure Amina Kabir suna inda ta ce tana auren maza biyu a lokaci guda.
Mijin Amina mai suna Kabir Muhammad Jibiya da ke zaune a cikin garin Jibiya shi ne ya kai Hindatu Yusuf kara a wannan kotu da ke karkashin jagoranci Mai shari’a Kabir Hamisu Bello, inda shi mai karar yake neman Hindatu da ta fito da miji na biyun da ta ce matarsa Amina na aure baya ga shi.
Samun damar shigar da wannan kara da Kabir ya yi a wannan kotu ya biyo bayan ikirarin da Hindatu ta yi ne na cewa Amina na auren wani mijin a cikin garin Katsina baya ga shi Kabir, a wani furuci da ta yi a wata karar da ta shigar a wannan kotu inda ta nemi a karbar mata bashin kudin da take bin Amina, ciki har da kudin buhun shinkafa hudu da ta ce Amina ta karba ta bai wa mijinta da ke Katsina mai suna Shamsu ya cika ya sayi mota.
A lokacin sauraren wannan kara da Hindatu ta shigar ne ya sa Kabir wanda yake cikin kotun a lokacin ya ji an ambaci cewa matarsa tana da wani mijin a Katsina baya ga shi,wanda nan take ya je ya shigar da kara inda yake kalubalantar Hindatu da cewa lallai sai ta nemo masa wancan miji na biyu da ta yi ikirarin matarsa Amina na aure a Katsina.
karar wadda Alkali Kabir ya fara saurare a ranar Talatar makon jiya, ta samu halartar wadda ake kara Hindatu Yusuf (wadda take kawar Amina ce) tare da mai kara Kabir Jibiya.
Bayan mai shigar da kara ya gabatar da kokensa a gaban kotu,Alkali ya tambayi Hindatu wadda ake kara cewa ta ji irin karar da ake yi mata kuma ta yi wancan furuci?
Wadda ake karar ta ce,hakika ta yi wannan furuci,kuma mijin da ta ce akwai a Katsina tabbas akwai shi, ta kuma san shi da kuma inda yake aiki, tare da sanin gidansa inda Aminar take zaune,ta kuma san haka ne saboda suna tare da Aminar.
A lokacin da take yi wa kotu bayani,Hindatu ta ce,ba ta da wata alaka ta jini da Amina sai ,dai alaka ta kasuwanci domin kawarta ce ta kusa.
Ta kara da cewa,”akwai wata rana za ni Funtuwa sai Amina ta kira ni a waya take gaya mani za a daura mata aure a nan Katsina,ni kuma na ce mata akwai matsala, amma sai ta ce ta san yadda za ta yi.
Ta ce \”Bayan kuma an daura auren ta shaida mani haka, inda na ce to Allah ya sa alheri za a ce ba, saboda an yi abin da ba daidai ba. Har wayau,da ni muka je babbar kasuwar Katsina inda ta yo sayayyar kayan kicin, wanda a nan ne ta shaida mani cewa uwar mijinta Shamsu wanda yake aiki a kotun da ke filin fayis a nan Katsina ta sayo mata katifa.”
Hindatu ta ci gaba da shaida wa kotu cewa,duk da ba ta san sunan unguwar da gidan Shamsu wanda ita Amina take ciki ba, amma za ta iya kai kanta gidan. Domin bayan Amina tana cikin gidan Shamsun a nan Katsina ta kirata ta waya,inda ita Hindatu ta bai wa mai Kurkurar (keken NAPEP) da ya dauke ta don yi masa kwatancen gidan ita Aminar. “Na kuma shiga cikin dakinta wanda yake ciki da falo ne.”
Hindatu ta ce,an daura auren Amina da Shamsu kimanin watanni biyar da suka wuce,ta kuma san wadansu daga cikin wadanda suka je wajen daura wannan auren, da suka hada da Jamilu (abokin Shamsun) da Zango da Muhammadu da sauransu, tare ma da shi wanda ya daura auren ita Aminar da Shamsu mai suna Baba Musa. “Duk na san haka ne saboda muna tare da Amina,kawata ce.”
Ta ci gaba da cewa,akwai wani rikicin da ya taba faruwa a tsakanin diyar ita Aminar da wata kawarsu inda har aka yanko sammacin kotu, wanda hakan ya sa ita abokiyar fadan ta ce muddin aka je kotu za a yi tone-tone.
Hindatun ce ta shiga tsakani, wanda hakan ya sanya mijin Aminar na Katsina ya shigar da kara a kotu ta 3 da ke Katsina a kan cewa Hindatu da kawarta za su bata wa matarsa suna a kan cewa za su yi mata tone-tonen cewa tana auren wani mijin daban. Amma sai aka sasanta su aka janye waccan karar, wadda a lokacin ne Amina ta fito da takardar shedar cewa mijinta na Jibiya ya sake ta, shi ya sa ta auri Shamsu.
Bayan wadda ake kara ta yi bayanin kariya ga dalilan cewa Amina na auren maza 2 a lokaci guda,Kabir mijin Amina ya ce, duk bai yarda da bayaninta ba.
Ya kuma musanta cewa matarsa tana zuwa wani wuri ta yi kwanaki ba a gidansa ba. Abin da kawai ya sani shi ne,kasancewar Amina na fama da matsalar ciwon sukari da hawan jini,su ne idan suka taso mata yake sa wa ta tafi ganin likita wanda a nan ne ake kwantar da ita har ta yi wadansu ‘yan kwanaki,adadin yadda likitan ya gani,sannan kuma ya sallamo ta. Kuma suna da rahoton duk abin da ke faruwa a asibitin, tun daga farko har karshe.
Kazalika Kabir ya ce,”mun samu matsala ne da ita a lokacin da zan sake wani auren, wanda hakan ya sa na sake ta har muka yi watanni 8 ba mu tare. Daga baya muka sake daidaitawa na biya sadaki aka sake daura mana aure (kimanin shekaru biyu a yanzu).
Wanda kuma ya daura mana auren farko a shekarar 1994 shi ne ya dauke ni tare da abokaina a cikin mota muka je garin da aka haifi mahaifinta inda muka samu magajin mahaifinta da kanen mahaifinta da sauran mutane, wanda a nan ne aka yanka mani sadakin da na biya,kuma shi wanda ya daura mana aure da ita tana budurwa shi ne ya sake daura mana auren.” Sai dai kuma Kabir ya amsa cewa,hakika Amina ta taba yin tafiya tsawon sati biyu ba ta gidansa.
Hindatu ta gabatar wa kotu da shaidanta na farko mai suna Alhaji Kabir Mohammad, mai shekaru 50, wanda ya ce suna unguwa daya da Shamsu ma’aikaci a Babbar kotun yanki (Upper Shari’a 1) ta daya da ke filin fayis a cikin garin Katsina, wato Unguwar Saulawa.
Mai gabatar da shedar ya ce,”kimanin sati 2 ke nan mun hadu a kotu ta 3 da ke kofar Soro,ni da Hindatu da Amina da kuma wata Rukayya inda aka yi karar cewa sun yi wa Amina kazafin cewa tana auren miji na 2 mai suna Shamsu.
Amina ta ba ni takardar shedar sakin aurenta,haka wata kotun yanki a garin Jibiya da ke jahar Katsina tana sauraren wata kara da ake zargin wata mata da bata wa wata matar aure Amina Kabir suna inda ta ce tana auren maza biyu a lokaci guda.
Mijin Amina mai suna Kabir Muhammad Jibiya da ke zaune a cikin garin Jibiya shi ne ya kai Hindatu Yusuf kara a wannan kotu da ke karkashin jagoranci Mai shari’a Kabir Hamisu Bello, inda shi mai karar yake neman Hindatu da ta fito da miji na biyun da ta ce matarsa Amina na aure baya ga shi.
Ya ce Amina ta ba ni takardar shedar sakin aurenta,haka kuma a gabana Shamsu ya yi ikirarin cewa, Amina matarsa ce,  har ma akwai shugaban kungiyar NARTO da sauran wadansu mutanen. Sannan kuma a gabana aka rubuta takardar cewa,sun janye batun cewa za su tona wa Amina asiri,su kuma suka janye karar da suka shigar.”
Alhaji Kabir ya sheda wa kotu cewa, duk da bai rike ranar da aka rubuta takardar sakin auren ba,amma ya rike cewa an rubuta,”ni Malam Kabir Jibiya na saki matata Amina saki daya.”
Ya ce duk ya san haka ne a lokacin da suke kokarin sasanta shi Shamsu mijin Amina da ya shigar da karar batanci ga matarsa da ya ce su Hindatu na son yi, kuma har suka ba Shamsun hakuri a kan cewa ya janye wannan karar, domin idan har haka ne wata rana Allah zai tona mata asiri, sai ga shi a yau an nemo shi don ya ba da sheda.
Da Alkali Kabir Hamisu Bello ya juya wajen Kabir mai kara don jin ko akwai abin da zai ce dangane da mai bayar da sheda na daya? Sai mai karar ya ce shi bai san mai bayar da shedar ba,haka kuma bai san abin da yake fadi ba.
“Amma na san Amina ta yi shari’a a Katsina sati biyun da suka wuce.” Lokacin da kotu ta nemi Amina idan tana cikin kotu da ta fito,mai kara ya nemi alfarmar cewa kafin a fito da ita yana son a nemo shi wancan mijin da aka ce akwai shi domin ya zo ya tabbatar da cewa Amina matarsa ce, tare da sauran shedu.
Alkalin kotun ya nemi Hindatu wadda ake kara da ta kawo wancan miji da ta ce Amina na da shi a cikin Katsina tare da sauran shedun da ta ce tana da su. Aka kuma sake daga sauraren karar zuwa ranar Litinin da ta gabata 9 ga watan Mayu,2016 don sauraren shedun.
A ranar Litinin din da ta gabata (9 ga watan Mayu) Hindatu ta je da dukkan shedun da aka ce ta je da su a wannan ranar, wadanda suka hada har da shi mijin da ake magana na biyu, wato Shamsu, domin jin ta bakinsu dangane da wancan ikirari da Hindatu ta yi na cewa Amina na auren mazaje biyu a lokaci guda.
To sai dai ba a samu zama domin ci gaba da sauraren shedun ba, saboda cikowar da kotun ta yi da jama’a ciki da wajen kotun, wanda hayaniyarsu ta sanya ba a jin maganar ko da na kusa da kai ne.
Hakan ya sa Alkalin kotun Alhaji Kabir Hamisu Bello ya dage zaman sauraren karar har zuwa ranar 30 ga watan Mayun 2016 bisa dalilan tsaro

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here