Inganta Sana\’ar Sayar Da Motoci Ne Burinmu – Na Birazil

  0
  1110

  Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  HADADDIYAR kungiyar masu sayar da motoci ta kasa reshen Jihar Kaduna sun bayyana cewa duk kokarin da suke yi suna fafutukar inganta sana\’ar ne domin kawar da batagarin da ka iya haifar da matsaloli a cikin harkar.

  Alhaji Muhammadu Nabirazil ne ya bayyana hakan a wajen babban taron kungiyar da ya gudana a Kaduna.

  Taron dai ya hada daukacin yayan kungiyar ne domin yi masu bita ta yadda za su san abin da doka ta ce a game da sana\’ar sayar da motoci.

  taron ya kuma samu halartar jama\’a daga cikin da wajen Jihar Kaduna da suka saurari muhimman jawabai daga lauyoyi, ma\’aikatan hukumar karbar haraji daga gwamnatin tarayya da na jihar Kaduna da kuma jami\’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC da sauran jama\’a da suka hadar da Yan majalisu na jiha Hakimin Unguwar Kanawa da sauransu.

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here