Ana Bincike Kan Karkatar Da Abincin \’Yan Gudun Hijira A Borno

0
969

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN jihar Borno  ta fara bincike kan zargin da ake yi wa wasu jami\’an hukumar agajin gaggawa ta jihar
da karkatar da abincin da hukumar NEMA ke kai wa \’yan gudun hijra.
A wata sanarwa, gwamnan jihar Borno,Kashim Shettima ya umarci hukumar \’yan sanda tare da
hukumar tsaro ta farin kaya da ke jihar da su gudanar da bincike sannan su kama duk wanda
ake zargi da hannu a batun.
Wannan dai ya biyo bayan hoton bidiyon da aka saka a wasu shafukan sada zumunta da ya
nuna wasu da ake kyautata zaton jami\’an hukumar agajin gaggawa ta Jihar Borno ne, su
na famar zuba shinkafar da hukumar NEMA ta kawo, a cikin wasu buhuna daban.
Malam Isa Gusau shi ne kakakin gwamnan jihar Borno,  ya fadi cewa duk wanda aka kama da hannu a batun
ba zai tsira ba, to sai dai kuma ya fara da bayyana shakkunsa kan al\’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here