Mayakan Boko Haram \’700 Sun Mika Wuya\’

0
1064

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram 700 ne suka mika
wuya ga gwamnati kawo yanzu.
Mayakan kungiyar, wacce ke kokarin kafa daular Musulunci a kasar, sun ajiye
makamansu ne a cikin wata shida da suka gabata, a cewar mai magana da yawun
rundunar tsaro .

 Birgediya Janar Rabe Abubakar ya shaida wa manema labarai  cewa mayakan sun fito ne daga sassa daban-daban na kasarnan da dama da ke fama da matsalar ta Boko Haram.
A baya dai gwamnatin Najeriya ta fito da wani shiri inda a karkashinsa za a rinka sauya wa
\’ya\’yan kungiyar tunani domin sake komawa su ci gaba da gudanar da rayuwarsu a cikin
jama\’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here