Solomon Arase Ya Yi Ritaya An Nada Sabon Sufeton \’Yan Sandan Nijeriya

0
1445

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Kpotum Idris, a matsayin
sabon Sufeton rundunar \’yan sanda na Najeriya.
An nada shi ne bayan saukar Solomon Arase, wanda ya kammala aiki bayan ya cika shekara
60 da haihuwa a duniya.
Kpotum zai maye gurbin Mista Solomon ne a matsayin shugaban \’yan sanda
Kafin sabon matsayinsa, Mista Kpotum ya rike matsayin mataimakin sufeton \’yan sandan mai
kula da ayyuka na a hedikwatar \’yan sandan da ke Abuja. Kpotum Idris dai mutumin jihar Naija ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here