Buhari Ya Gargadi Fayose Kan Matarsa A\’isha

  0
  1086

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  SHUGABA Muhammadu Buhari ya yi watsi da wani \’kage\’ da Gwamnan Jjihar Ekiti Ayo Fayose ya yi kan matarsa A\’isha
  Buhari, inda ya danganta ta da wata badakalar cin hanci a Amurka.
  Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya ce bai kamata a bar Fayose ya dulmiyar da \’yan Najeriya da zantukansa \”na
  karya\” ba.
  Muna \”gargadi da kakkausar murya ga Mista Fayose ya san cewa A\’isha Buhari na da damar kare mutuncinta\”.
  Garba Shehu ya kara da cewa ya kamata Gwamnan ya shiga \”taitayinsa ya san cewa bambancin siyasa ba lasisi ba ne na cin zarafin
  jama\’a\”.
  A ranar Litinin ne Gwamna Fayose ya shaida wa kafofin yada labarai cewa A\’isha Buhari na da hannu a badakalar cin hanci da ta hada da
  wani dan majalisar dokokin Amurka William Jefferson, da aka yanke wa hukunci a shekarar 2009.
  Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta ce, A\’isha Buhari ba ta da hannu ko wata alaka da wannan badakala da Fayose ya danganta ta da ita.
  Gwamna Ayo Fayose na sahun gaba a jerin \’yan adawar da ke sukar manufofin gwamnatin Buhari da kuma jam\’iyyar APC mai mulki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here