Duk Da Matsalar Boko Haram Ba\’A Bin Gwamnatin Jihar Borno Bashin Albashi

0
1245

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNAN Jihar Borno Alhaji Kashim Shetima, ya bayyana cewa duk da matsalar da yankin arewa maso Gabas ke fuskanta na rashin tsaro amma ya zuwa yanzu ya biya albashin ma\’aikata baki daya.

Idan aka yi la\’akari da irin yadda Najeriya ke ciki da Jihohi, Kananan hukumomi basa iya biyan albashi na tsawon wasu watanni, lamarin da ke neman zama ruwan dare sakamakon hare haren da yan ta\’addan yankin Neja Delta ke kaiwa bututun mai da aka shimfida a fadin kasa baki daya.

Sai kuma halin da ake ciki na tabarbarewar farashin mai a duniya Wanda ya haifar da karancin kudin da kasashe suke samu musamman Najeriya da ta dogara a kan kudin Man Fetur domin biyan albashi da kuma tafiyar da harkokin gwamnati da na al\’amuran yau da kullum.

Bisa wadannan dalilai za\’a iya cewa gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Alhaji Kashim Shetima ta yi rawar gani musamman ganin yadda Jihohin da suka fi jiharsa samun kudi daga kason gwamnatin tarayya da ake takama da shi amma a yanzu irin wadannan jihohi wasu sun kasa biyan albashin watannai Shida,Bakwai, wasu kananan hukumomin na yankin Neja Delta sun kwashe shekara daya babu albashi.

Amma ita Jihar Borno duk da irin yadda aka kwashe shekaru ana yakin Boko Haram sai gashi Kashim Shetima ya biya albashin baki daya lallai wannan abin a yaba ne tare da jinjinar ban girma, saboda idan da wasu ne za\’a ce ragowar yaki ne don haka ba komai.

Kuma duk da haka ko a watannan na Azumi sai da gwamnatin Kashim Shetima na Borno ya rabawa jama\’a shinkafar azumi domin a samu saukin halin da ake ciki kamar yadda kowa ya sani domin hantsi ne leka gidan kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here