Gwamnatin Tarayya Ta Sallami Likitocin Da Ke Yajin Aiki

0
1018

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta sallami likitocin da ke samun horo na kwarewa a asbitocin
gwamnatin tarayya wato (resident doctors).
Ministan kiwon lafiya, Isaac Adewole ya ce daina zuwa aiki da wasu daga cikin
likitocin suka yi ya saba wa dokar tsarin aikin gwamnati.
Likitocin, wadanda ke koyon aikin a sassan kasar da dama, na yajin aiki ne dangane da
batun albashi.
A wata sanarwa da ministan ya fitar, ya umarci shugabannin cibiyoyin kiwon lafiya na
gwamnatin tarayya su maye gurbin likitocin da ke yajin aiki.
\”Abin takaici ne a ce likitocin sun bar wuraren aikinsu duk da cewa, ana tattaunawa da
wakilan kungiyarsu a kan korafin da suke da shi,\” a cewar Misata Adewole.
A lokacin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ma likitocin sun yi irin wannan rikici
da gwamnati, inda aka bayar da sanarwar sallamarsu gaba daya, amma daga bisani aka
dawo da su bakin aiki.
Wadannan likitoci na taka rawa sosai a fannin kiwon lafiya a kasar, kuma masu sharhi na
ganin matakin ka iya kara lalata al\’amura a fannin kiwon lafiyar kasar.
Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara na kokarin shiga tsakanin likitocin da
kuma ma\’aikatar lafiya domin shawo kan matsalar amma abin ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here