Boko Haram: \’Mutum 200 Sun Mutu Saboda Yunwa\’

0
1288

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR likitoci masu bayar da agaji ta duniya Medicins San Frontier, MSF ta ce kusan mutum dari biyu ne wadanda suka
tsere wa rikicin Boko Haram  suka mutu saboda matsananciyar yunwa da kishirwa a watan da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce akwai bukatar agajin gaggawa a sansanin \’yan gudun hijra da ke Bama, wanda yanzu haka
yake dauke da \’yan gudun hijra fiye da dubu ashirin.
Kungiyar ta kara da cewa mafi akasarin \’yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin yanayi, kuma yawancin su yara ne wadanda da an duba
lafiyarsu za a ga cewa suna fama da rashin abinci mai gina jiki.
Wata kididdiga da majalisar dinkin duniya ta yi ta nuna cewa fadan da ake yi tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da kuma sojojin Najeriya
ya tilasta wa mutane kusan miliyan biyu barin gidajensu.
\’Babu alaka tsakanin Boko Haram da IS\’ Boko Haram ta sace wasu mata a Damboa
MSF ta ce mazauna sansanin da dama na cikin matukar kaduwa kuma yaro daya cikin biyar na fama da cutar tamowa.
A cewarta, mutanen da suka rasa matsugunansu a Bama sun ce ana binne mutum kusan 30 a kullum wadanda suka mutu
sanadiyar yunwa ko cuta.
Kungiyar ta kara da cewa kodayake abu ne mai matukar hadari a yi tafiya ta kan hanyoyin yankin, amma jami\’anta sun je Bama ranar
Talata. Ta ce hakan ya faru ne bayan sun samu rakiyar dakarun sojojin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here