AN KAMA WANI MUTUM DA KE LALATA DA \’YA\’YANSA MATA 3

0
765

Daga Usman Nasidi

WADANSU ’yan mata uku sun kai mahaifinsu mai suna Akila Likita mai kimanin shekara 47 da ke aikin gadi a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya kara ofishin ’yan sanda da ke Danmagaji saboda yawan lalata da yake yi da su.
’Yan mata uku da mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu dukkansu suna zaune ne a gida daya a Wusasa a karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.
’Yan matan da suka hada da babbarsu Comfort Akila da mai bi mata Felicia Akila da ta ukunsu Faith Akila, sun kai mahaifinsu kara ofishin ’yan sandan ne inda suka ce mahaifinsu kullum yana kwantawa da daya daga cikinsu.
Sun ce bayan ya gama saduwa da dayansu sai ya fito da wani farin kyalle ya share al’aurarsa kuma ya share nasu, wanda hakan ke sanya su cikin damuwa, ganin yadda mahaifinsu ne ke yi musu hakan.
A cewarsu, tun suna boyewa har abin dai ya gagara suka sanar da mahaifiyarsu ga abin da mahaifinsu ke yi musu kuma suna zargin wannan abu tsafi ne.
Sun ce mahaifiyarsu ta sanar da kanwarta,wadda ta ce ba za su yarda wannan abu ya rika faruwa a danginsu ba, don haka suka gabatar da shi ga ’yan sanda.
Bayan kammala binciken da ’yan sanda suka yi ne DPO din Danmagaji, Kassim Abdul ya ce a tura su kotu domin a yi musu shari’a.
A Babbar kotun Majistare da ke kofar Fada,Zariya, inda aka gurfanar da Akila Likita, mai gabatar da kara, Sufeta Sarki Abdullahi ya karanta tuhumar da ake yi wa mahaifin ’yan matan, kuma ya amsa cewa lallai haka ya faru.
Alkalin kotun Majistare Umar Bature ya ce kotunsa ba ta da hurumin sauraren shari’ar kuma ya tura shi zaman jiran shari’a na wata daya tare da tura batun ga ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna domin daukar mataki na gaba.
Wanda ake zargin kafin a wuce da shi, ya bayyana cewa  ya yi nadamar abin da ya aikata, kuma wannan sharrin Shaidan ne don  wani abokinsa ne ya kai shi wajen wani malaminsa cewa za a yi min kudi.
Ya ce abokin nawa sunansa dahiru kuma yana zaune ne a Gyallesu, bayan na yi lalata da ’ya’yana ukun, ina share azzakarina da farin kyallen da ya ba ni ne da al’aurar ’ya’yana domin haka suka umarce ni in yi har na tsawon wani lokaci kuma bayan na kammala in kai masu kyallen amma yanzu abokin nawa ya gudu zuwa Obajana ya bar ni ba tare da samun kudin ba.
Don haka na yi nadama, kuma ’ya’yan nawa ina tare da mahaifiyarsu a zaman aure kusan shekararmu 35, don haka ina roko ta yafe min haka ’ya’yan nawa, ka gan su muna tare a kotun yanzun nan na gama rokonsu su yafe min wannan sharrin Shaidan ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here