An Kai Harin Bam A Kusa Da Masallacin Annabi

0
1289

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RAHOTANNI daga birnin Madina na kasar Saudi Arabiya na cewa an kai harin kunar bakin wake a kusa da masallacin Annabi SAW wato dai inda kabarinsa yake.

Indai za a iya tunawa wannan harin shi ne kashi na uku da aka samu a ranar Litinin din nan inda aka kai na farko a ofishin Jakadancin Amurka a birnin Jidda da masallacin Shi\’a a garin Qatif sai kuma na masallacin Annabi.

Rahotannin sun yi bayanin cewa an ga wani faifan bidiyo a kusa da wajen wata mota na cin wuta sai jami\’an tsaro a kwance su biyu.

Babu dai rahoton mutanen da suka rasa rayukansu ko wani jawabi daga hukumomin kasar ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here