Ebola Ya Fice Daga Gasar Damben Mota A Kaduna

  0
  6771

  M.I Abdullahi Daga Kaduna

  SHARARREN Dan Damben gargajiya nan Abdurrazaq da ake yi wa lakabi da Ebola ya fice daga gasar cin motar da aka sa wa yan wasan Dambe a Kaduna.

  Kamar dai yadda aka sani shi wannan Ebola ya samu nasarar lashe gasar da aka yi a Kano inda ya samu nasarar lashe wata mota.

  Alkalin wasan da ke alkalancin gasar cin mota a Kaduna mai suna Sarkin Gida Na Jafaru Kura, tare da  Shagon Amadi, Gunnari ke taimakawa alkalin was an da suke rike da tutoci a hannunsu.

  An dai fara damben cin gasar mortar ne da misalin karfe biyar da rabi na Yammacin jiya Litinin a filin wasa na yan wake da ke Unguwar Magadishu cikin garin Kaduna.

  An fara ne da rubuta sunayen yan wasa a cikin takarda inda aka kudin dine sai yan wasa su dauka domin sanin Wanda za su kara da shi daga cikin mutane biyar biyar da bangaren kudu da na Arewa suka zabo domin a fafata.

  An kuma saka wa kowane Dan wasan da zai kara da Dan uwansa kyalle a kugunsa yan arewa Jan kyalle su kuma Kudawa kyalle mai launin dorawa.

  An fara ne da wasa tsakanin shagon shagon Buhari da kuma Dan Sama\’ila da ake wa lakabi Dan shagon Alabo.

  Sai kuma Wasa na biyu tsakanin Shagon Buhari da Ebola inda aka yi turmi uku babu kisa, wanda hakan yasa suka dauki takarda a tsakaninsu nan take Ebola ya dauki Mara cin wato (no) da ta tabbatar da an cire shi daga gasar duk kuwa da cewa Tauraruwarsa ce ke haskawa a yanzu da ake ganin zai lashe gasar kamar yadda ya yi a Kano.

  An kuma samu kwantan wasa Na uku tsakanin Bahagon Sisko da Ali KANIN Bello saboda da Dare ya yi.

  Indai za\’a iya tunawa Ali Kanin Bello ne ya fara kai Ebola kasa a Kaduna Mutumin da ya kwashe sama da shekara daya bai je kasa ba a duk fadin Najeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here