Nicaragua: Ortega Ya Dauki Matarsa A Matsayin Mataimakiyarsa 

0
1109

Mustapha I Abdullahi Kaduna

\"NicaraguanImageAFP
ImageMr Ortega a hagu tare da matarsa Rosario Murillo  a Dama lokacin da suka gabatar da takardun takararsu a babban birnin Managua a ranar Talata. 

SHUGABAN kasar Nicaragua Daniel Ortega ya bayyana sunan matarsa a matsayin wadda za su yi takarar shugabancin kasar tare

Ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake son jama\’a su zabe shi a karo na Uku.

Ita dai matar tasa mai suna Rosario Murillo, ta samu wani matsayin musamman a gwamnatin da mijin ke yi wa jagoranci inda take rike da ofishin mai magana da yawun gwamnatin, lamarin da ya bata damar ake gani kamar suna raba iko ne da mijin.

Tana bayyana a kafar Talabijin a kowace rana .

Yan adawar siyasar kasar na sukan lamarin da cewa kamar ana tafiyar da kayan gado ko wani abu na kashin kansa a matsayinsa na shugaban kasa.

Shi dai Daniel Ortega da jam\’iyyarsa sun raba mulki ne a shekarar 1990 amma kuma a samu nasara a shekarar 2007 don haka yana bukatar a yanzu su lashe zabe shi da matarsa kuma uwar yayansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here