An Hana Ganduje Da Kwankwaso Tarukan Siyasa

  0
  1155

   

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  Rundunar \’yan sanda a jihar Kano ta dakatar da gwamnatin jihar da kuma gidauniyar Kwankwasiyya tarukan da suka shirya yi daban-daban a jihar a ranar Asabar mai zuwa.
  Tun da farko dai gidauniyar Kwankwasiyya ta shirya taron bikin auren zawarawa da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki nauyi a karshen mako.
  Ita ma a nata bangaren, gamnatin jihar ta shirya wani taro na tallafawa matasa a karshen makon a dakin wasanni na Sani Abacha dake cikin birnin.
  Gidauniyar ta tsohon gwamnan jihar, Injiniya Rabi\’u Musa kwankwaso ta shirya aurar da zawarawa 100 ne a filin polo shi ma a birnin na Kano.
  A wata sanarwa da rundunar \’yan sandan jihar ta futar ta ce ta dakatar da duka tarukan ne sabo da wasu bayanan sirri da ke cewa wasu za su kawo yamutsi.
  Sanarwar \’yan sandan ta ce nan gaba kwamishinan \’yan sandan jihar zai kira duka bangarorin da lamarin ya shafa taro, da nufin nemo mafuta kan batun.
  Dangantaka ta kara tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun a watan Maris din da ya gabata, bayan mutuwar mahaifiyar gwamnan mai ci yanzu.
  Zuwa yanzu dai bangarorin biyu ba su mai da martani kan batun ba.
  An fara aurar da zawara ne a Kano a lokacin gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso, kuma a yanzu haka gwamnatin jihar mai ci ta Abdulllahi Umar Ganduje tana tanatance daruruwan mata domin aurar da su.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here