PDP Ta ƙara Wa Kwamitin Maƙarfi Wa\’adi Amma Har Yau Tana Tsaka Mai Wuya

  0
  7798

   

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  BANGAREN da ke goyon bayan shugabancin Ahmad Maƙarfi a jam\’iyyar PDP ya ɗage babban taron jam\’iyyar da aka shirya gudanarwa a birnin Fatakwal, sannan ya ƙara wa Makarfi  wa\’adin shekara guda.
  Jam\’iyyar ta ce tana so ta warware duka wasu batutuwan shri\’a da ta ke fuskanta cikin shekarar.
  Shugaban shirya kwamitin taron wanda kuma shi ne gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike shi ne ya bayyana matakin.
  Hukuncin ɗage taron dai ya biyo bayan gazawar da bangaren ya yi na gudanar da babban taron da ya shirya gudanarawa a jihar Rivers, bayan wata babar kotun tarayya a Abuja ta dakatar da taron.
  Tun da farko dai sojoji da \’yan sanda sun killace filin wasanni na Sharks, wajen da aka shirya gudanar da taro

  A wata sabuwa kuma, jam\’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta samu kanta a cikin tsaka mai wuya bayan manyan kotuna biyu na kasar sun bayar da umarni masu cin karo da juna kan shugabancinta.
  Wata babbar kotu a Abuja ta haramta wa jam\’iyyar yin babban taronta da za a yi a fatakwal a ranar Laraba.
  Hakan na zuwa ne bayan wata babbar kotun da ke zamanta a Fatakwal ta bayar da umarnin a yi taron.
  Tun bayan da PDP ta rasa mulkin Najeriya a shekarar 2015 ne jam\’iyyar ke fuskantar rikici na cikin gida, lamarin da ke kara dagulewa.
  Hakazalika yunkurin daidaita bagarorin da ba sa ga maciji da juna na Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi ya ci tura.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here