Sojojin Sama Sun Musanta Kashe \’Yan Matan Chibok

0
1284

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojan sama ta Najeriya ta musanta ikirarin da Boko Haram ta yi na cewa, hare-haren da suke kai wa sun kashe wasu daga cikin \’yan matan Chibok.
Rundunar sojan tana mayar da martani ne ga bidioyon da Boko Haram ta fitar ranar Lahadin da ta wuce, inda ta yi ikirarin.
A shafinta na Facebook rundunar sojan ta kuma ce, \’yan Boko Haram sun ɗauko hotunan wasu gawawwaki ne suka tsara a bidiyon.
Rundunar ta kara da cewa, wurin da \’yan Boko Haram suka nuna bai yi kama da wurin da aka kai hari ta sama ba.
Rundunar ta kuma sanya bidiyo a shafinta na Facebook da ya nuna yadda ta ke amfani da na\’urori masu hangen nesa dake fayyace mayaƙan Boko Haram kafin a kai musu hari ta sama.
Bidiyon ya kuma nuna yadda ake bincike mai zurfi, da tattara bayanan sirri kafin a kai kowanne hari da jiragen yaki
\”Muna da na\’urori na zamani da matakai masu yawa dake tantancewa sosai kafin mu kai hari ta sama da rana, ko cikin dare. A duk lokacin da muke da shakku to muna dakatar da kai hari har sai mun tabbatar da abokan gaba ne kafin mu kai hari ta sama\”, in ji rundunar sojan saman ta Najeriyar.
Dan haka ne sojan saman suka ce, \’yan Boko Haram sun yi amfani da bidiyon da suka fitar ne domin yaudarar jama\’a.
Hare-hare ta sama dai sun yi tasiri wajen cin karfin \’yan kungiyar ta Boko Haram.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here