Awarar Nama Da Kwai

0
2443

Daga Hauwa Zubairu

\’\’YAN uwana mata barkanmu da wannan lokaci, kuma sannunmu da ayyukan alheri ga masu gidajenmu, wato mazajenmu. Ina kara jinjina sosai gare mu da ma su kansu mazajen namu da suke iyakacin kokarinsu na nemo wa iyalansu halaliya domin su ciyar da su baki daya. Allah nake rook ya kara yalwata su daga cikin taskarSa,amin.

To, a yau zan so ne in fara da wani dan abinci na kwalama, wato ‘Awarar nama da kwai’. Uwargida da zarar kina son ki yi wa maigida irin wannan awarar, to, za ki tanaji danyar awararki, sa’annan ki fasa kwanki ki cakudeta da kwan, sai ki sanya ta a cikin leda ki mayar da ita kan wuta tamkar za ki dafa alalen leda, idan ta dahu tubus sai ki fito da ita dama kina da dakakken namanki na kaza ne ko na rago ko na Saniya ne sai ki kara cakude awarar nan da naman nan da wasu kwayayen kaza kuma, sai ki mayar a wuta ya dahu sosai.

Da zarar ya kara dahuwa sai ki sauke shi ki yanka shi girman da kike bukata, sai ki tanaji ruwan sanyinki ki ajiye wa maigida, ki sha kallo da jiran santi, shin nama ne yake ci ko kwai ne koko mene ne?

\"\"

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here