Da Mutane Na Ganin Abubuwan Da Muka Gani Da Ba Su Yi Kukan Tsadar Kaya Ba – Sadiq Abubakar

0
1254

M I Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN rundunar sojojin sama na tarayyar Najeriya Sadiq Abubakar, ya fito fili ya bayyana cewa da jama\’a Na ganin ainihin irin abubuwan da suke gani da babu wanda zai yi maganar ko kukan cewa akwai tsadar abubuwa a kasar nan ba.

Shugaban sojin saman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Tashar Talbijin ta NTA mai watsa shirye shiryen ta da harshen Hausa.

Inda ya ci gaba da cewa hakika a kokarinsu Na gudanar da aiki sun yi gane gane da damar gaske wanda da jama\’a suna ganin irin abubuwan da ke faruwa da ba a yi kukan tsada ba.

Don haka ya kara kira ga daukacin yan Najeriya da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga rundunonin soja da dukkan sauran rundunonin tsaro domin samun nasara.

\”Mun kirkiro da wani shiri ga jami\’an da ke aiki ta yadda mutum zai iya mallakar gida wanda hakan ba karamin abu bane da zai amfani mutum shi da iyalinsa ko bayan barin aiki\”.

Ya ce ko a kwanan baya sai da wasu tsageru suka bullo a yankin Jihar Legas amma da suka tashi tsaye nan da nan suka yi maganinsu ba bata lokaci.

A saboda haka duk inda wani ko wasu tsageru suke a fadin kasar nan sun lashi Takobin yin maganinsu cikin hanzari domin kasa ta ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here