Duk Mai Son Samun Nasara Sai Ya Girmama Jama\’a

0
1261

M I Abdullahi Daga Kaduna

WATA fitacciyar yar wasan fina finai Rahama Hassan, ta bayyana cewa lallai duk mai son samun nasara a rayuwarsa dole ne ya rika ganin girma daraja da kuma martabar jama\’a.

Ta ce hakan kuma ya dace ya faru koda mutum ya girme ka ko kuma yana kasa da kai ko shi tsaranka ne domin yin haka zai bayar da gudunmawa wajen samun fahimtar juna a tsakaninku ga dukkan al\’amuran da zaku yi na rayuwa.

Rahama Hassan, ta bayyana hakan ne a lokacin da ake tattaunawa da ita a wani shirin gidan Talbijin na farin wata.

Rahama, ta ci gaba da cewa tun tana makaranta take yin wasan kwaikwayo don haka kusan duk kokarin da take yi a wajen fim dama can mafi yawa da abin ta taje don haka ta kanyi fice kusan kowa ne lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here