Sa-In-Sa Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje Ba Ta Yi Mana Dadi – Dan Gwari

  0
  1020

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

   

  WANI jigo a jam\’iyyar APC dake yankin karamar hukumar Fagge ta jihar Kano Alhaji Usman Dan Gwari yace magoya bayan  tsohon Gwamnan jihar kuma Sanatan Kano ta tsakiya Dokta Rabi\”u Musa Kwankwaso da kuma Gwamna mai ci wato Dokta Abdullahi Umar Ganduje  ba sa jin dadin rikicin siyasar da bangarorin biyu ke gwabzawa, inda ya bukace su da su dinke barakar da ke tsakaninsu domin ci gaban jihar.

  Alhaji Dan Gwari yayi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu, inda ya yi kira ga shugabannin biyu da su yi waiwaye kan tsohuwar tafiyar su wadda take da tsohon tarihi maimakon yin rikici na cikin gida wanda a cewarsa, ko kadan ba zai taimaki Jihar Kano ba a tafiya irin ta siyasar wannan lokaci.

  Sannan ya nunar da cewa yana da kyau tsohon Gwamna Kwankwaso da Gwamna  Ganduje su sani cewa su ne ake kallo a matsayin iyaye a siyasar Jihar Kano, don haka su yi hakuri su hada karfi wajen bunkasa Jihar Kano maimakon rikicin da suke yi na ciKin gida wanda bai yi wa dukkanin magoya bayan su dadi ba.

  Daga karshe, Alhaji Usman Dan Gwari ya yi fatar cewa nan gaba kadan tsohon Gwamnan da kuma Gwamna mai ci za su yi wani abu wanda zai nuna wa magoya bayansu cewa har yanzu suna tare kamar yadda suke a lokutan baya.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here