YA KASHE MATARSA DA ‘YARSA DA MATAR FASTO DA TABARYA

0
1038

Daga Usman Nasidi

ANA zargin wani mutum mai suna Taiwo Adio na cocin Imani Baptist da ke zaune a Unguwar Tsohon Filin Jirgin Sama na Sakkwato da ke karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a Jihar Sakkwato da kashe matarsa da ‘yarsa da matar limamin cocinsu (Fasto) da kawarta da ta kawo mata ziyara.
Wanda ake zargi ya dauki tabaryar da matarsa ke kirba doya da ita ne a lokacin da matar take cikin daki kafin ta yi aune ya buga mata ita a kai, ta fadi sannan ya buga wa ‘yar sannan ya wuce dakin da matar Faston ke zaune da kawarta ya same su ya buge a nan take dukkansu suka rasu.
Wani mutum da wakilinmu ya tarar a kofar gidan da aka yi aika-aikar kafin ‘yan sanda su wuce da gawarwakin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami\’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, ya ce, Mista Taiwo Adio ya samu matsala ne bayan sace shi da aka yi, kuma da ya dawo
ya daina yi wa mutane magana, bai ce wa kowa komai sai dai ya yi shiru a kodayaushe
Wani mamban cocinsu mai suna Oyelike Samson ya zargi Taiwo Adio da kashe matan da tabarya da misalin karfe 8:00 na dare a wannan mummunar ranar ta Asabar.
Duk kokarin haduwa da Faston da aka kashe matarsa da wakilinmu ya yi, ya ci tura saboda ba ya cocin kuma gidan da suke zaune a rufe yake.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar sakkwato Almustafa Sani ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce wanda ake zargi yana hannunsu tare da tabaryar da ya kashe matan su hudu, ana yi masa tambayoyi ko a sami wani abin kamawa daga bakinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here