Hukumar Zabe INEC Ta Yi Wa Jama’ar Kogi Hawan Kawara – Wada

0
1026

 

Daga Zubair A Sada

TSOHON Gwamnan Jihar Kogi, Idris Wada a yau Talata ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta INEC da yin hawan kawara bisa hakkokin jama’ar Jihar Kogi. Idris Wada wanda shi ne dan takarar kujerar gwamnan jihar a tutar PDP ya ce INEC din ta yi kuskure a yayin da ta bayyana cewa, Yahaya Bello shi ne ya lashe zaben na Gwamnan jihar.

Lauyan da yake tsaya wa Idris Wada Chris Uche ne ya sanar da haka a yayin da ake sauraron shari’ar da suka shigar a kotu inda ya ba da misali da sashe na 33 da na 35 da 36 na dokokin zabe, inda ya ce aikin ba da satifiket da INEC ta yi kuskure ne.

Lauya Uche ya ce, kuskure ne a ba mutumin da ke da kashi 5 kacal na kuri’un jama’ar da suka yi zabe. Ya ci gaba da cewa, ‘’Yahaya Bello bako ne kuma ya zamanto masaukinsa a halin yanzu gidan gwamnatin Jihar Kogi ba a bisa ka’ida ba’’.

Ya ce abin da INEC ya dace ta yi shi ne ta sanya ranar sabon zabe, idan da ta yi haka ba za a kai zuwa ga wannan matsala ba’’. Ya kuma yi Allah wadai da ‘’gadon’’ kuri’un Abubakar dukansu da APC ta yi.

Da yake maida martanin jawaban da aka yi, Lauyan wanda ake kara, Joseph Daudu ya nemi kotun ne ta yi watsi da batun da lauyoyin mai kara suka yi, ya yi nuni da cewa, babu dalilin da za su yi ta kawo sashe-sashe na kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ga shi ba su san yadda INEC ta gabatar da zaben tare da tabbatar da Gwamnan Jihar Kogi ba.

Ya ce ‘’mai kara bai sani ko gane cewa zaben watan Nuwamba da na Disambar 2015 zabe ne guda daya ba. Na watan Nuwamba an bayyana rashin kammaluwarsa inda aka kammala shi zaben a watan Disamba. To yaya zai ce wanda nake tsaya masa a shari’ar ya sami kashi 5 ne kacal na kuri’un?

Lauya Daudu ya ci gaba da cewa, sanin kowa ne INEC ta nemi a sami makwafin dan takarar na APC dalilin rasuwar wanda yake takarar, shi ne jam’iyyar ta zabo Bello, ka ga da wannan ne ya ci gadon kuri’un mamacin.

Daga karshen al\’amarin duka Babbar Kotun kasa da ke zamanta a Kogi ta yanke shari\’ar inda ta bar wa Gwamna Yahaya Bello kujerarsa ta mulkin Jihar ta Kogi bayan ta yi watsi da hujjojin masu kara inda ta ce hujjojin nasu ba su da karfin da za su karbu a wajen masu shari\’a.

Magoya bayan Gwamna Yahaya Bello da jama\’arsa sun yi wa kotun kawanya domin sauraron shari\’ar, kuma sun yi bukukuwan murna har zuwa cikin gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here