Ma’aikatn Bas-Bas A Birnin Tarayya Suna Yajin Aiki

  0
  869

   

  Daga Hauwa Zubairu

  AL’UMMA mazauna babban birnin tarayya Abuja sun nuna damuwarsu tare da bakin cikinsu a kan yajin aikin da ma’aikatan bas-bas na Abuja suke yi harna tsawon wata daya, al’amarin da ya jawo wa al’umma tsanani da wahalar zirga-zirgarsu a birnin.

  Kamfanin bas-bas din na Abuja an kafa shi ne tun a shekarar 1984 da yake jigilar al’ummar birnin tarayya da aka fi saninsa da bas-bas din El-Rufai wanda aka rada wa motocin sunan tsohon ministan FCT, wato Gwamnan jihar Kaduna a halin yanzu, Malam Nasir El-Rufai.

  Ma’aikatan bas-bas din sun tafi yajin aiki ne a watan jiya bayan bangaren gwamnatin da ke kula da su ta gaza biyansu albashinsu na watanni biyar. Sai dai ana sa ran za a zauna da shugabannin ma’aikatan domin shawo kan lamarin.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here