PDP: Sheriff da Makarfi za su sasanta

  0
  971

   

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  KOKOWAR shugabancin jam\’iyyar PDP da Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Ali Modu Sheriff sun sha alwashin sasantawa.
  Mutanen dai sun dade suna ja-in-ja game da shugabancin jam\’iyyar, lamarin da ya kai su ga kotuna daban-daban.
  Sai dai bangarorin biyu sun shaida wa manema labarai  cewa za su sasanta da juna domin kawo karshen kai-ruwa-ranar da suka kwashe wata da watanni suna yi.
  Jam\’iyyar ta PDP dai ta fada cikin rikici ne tun bayan kayen da ta sha a zaben shugabancin  shekarar 2015.
  Masu sharhi a kan harkokin siyasar kasar sun ce rashin hada kai tsakanin \’yan jam\’iyyar ta PDP wani babban koma-baya ne ga dimokuradiyya kasancewa babu jam\’iyyar da za ta soki gwamnatin kasar wacce ta kwace mulki daga PDP.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here