AN GANO BAMABAMAI 67 DA BOKO HARAM TA BIRNE A BARIKI

0
955

Daga USMAN NASIDI

RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Borno ta ce ta gano kuma ta lalata bama-bamai akalla guda 67 a barikin soja da ke garin Bama wanda a baya yake hannun yan kungiyar Boko Haram.
kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chukwu yayin wata hira da ‘yan jaridu yana cewa da yammacin ranar 25 ga watan Satumba ne jami’anmu na musamman masu kula da bam suka lalata bama-bamai 67 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka binne a barikin.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa “A lokacin da Gwamnan da mukarrabansa ke kokarin komawa su tare a garin Bama don sa ido kan batun aikace-aikacen sake gina garin, sai na sanya kwararrun jami’anmu na sashi daban-daban kamar cikin ayarinsa don su raka shi.
A yayin gudanar da aikin sake gina barikin sojoji na Bama shi ne sojojin da ke wajen suka ga bama-bamai guda 67, inda ba su yi wata-wata ba suka kira jami’an ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sanda Damian ya kara da cewa “muna da yakinin ‘yan ta’addan sun binne bama-baman ne don idan sojoji sun dawo su tashi da su. Na sanya kwararrun jami’anmu suka hako bama-baman, kuma suka lalata su, daga nan ne aka ci gaba da aikin gine ginen.”
Sa’annan ya tabbatar da zuba tarin ‘yan sanda a garin Bama don samar da tsaro a garin tare da tabbatar da an kula da yankunan da mayakan rundunar sojan kasa suka kwato daga hannun yan Boko haram.
Daga karshe kwamishinan ya karkare da cewa “a yanzu haka mun watso a kananan hukumomi da dama don tabbatar da tsaro, akwai jami’anmu a karamar hukumar Konduga, gari ne a tsakanin Bama da Maiduguri. Haka ma a Munguno, gari ne a tsakanin Bama da Baga.
Har yanzu sojoji suna karon-batta da ‘yan ta’adda a kan iyakar kasar nan da kasar Chadi, amma an kwato garin a hannunsu, illa dai wasu ‘yan kauyuka da ba za a rasa ba.” Inji Damian.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here