Boko Haram Ta Kafa Tuta A Wasu Kauyuka Uku A Borno

0
977

 

Rabo Haladu Daga  Kaduna

WATA majiyar soji da fararan hula na cewa mayakan Boko Haram sun kafa tutocinsu a wasu kauyuka uku a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa mayakan sun yanka mutane takwas, ciki har da wani dagaci, a lokacin da suka kai hare-haren a yammacin ranar Litinin.
Kauyukan na Kubirivour, Boftari and Kuburmbalah na kusa da garin Chibok ne, inda aka sace \’yan makaranta fiye da 200 a shekarar 2014.
Akalla mutane 17 ne aka jikkata a hare-haren.
Wata majiya ta ce har yanzu mayakan Boko Haram na rike da wasu garuruwa.
A ranar Lahadi ne, sojojin Najeriya suka kwato wasu garuruwa daga hannun mayaka.
Sai dai rahotannin sun ce sun sake damara inda suka sake kwace ikon wasu garuruwa.
Harin na baya-bayan nan na nuna yadda har yanzu kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da zama barazana ga kasar nan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here