AN KAMA WADANSU DA AKE ZARGI DA ZAMA \’YAN KUNGIYAR BOKO HARAM

0
1043

Daga USMAN nasidi

A safiyar shekaranjiya Laraba ne dakarun Operation Lafiya Dole tare da taimakon ‘yan banga suka kama wasu mutane.uku a kasuwar shanu da ke Maiduguri wadanda ake zargin mambobin Boko Haram ne.
Wadanda ake zargin sun hada da Abba Go Dallagio, Abba Fanned da Alhaji Nwariye.
A yayin da ake gudanar da bincike a kansu, sun yi ikrarin cewa sun shigo kasuwar ne ta yankin Mafa da shanu guda 200 domin su sayar.
Sun kuma kara da cewa suna daga cikin masu.taimaka wa Boko Haram wajen sayar musu da shanu.
Hakazalika a wani labari makamancin haka ma, sojojin sun kama wani jakada kuma dan leken asirin ‘yan Boko Haram mai suna Alhaji Ajid Umar a kasuwar shanun.
An gano shanu kimanin 170 ta hannunsa kuma yanzu haka ana kan ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here