DIREBAN BRT A JIHAR LEGAS YA TAIMAKA WA WATA TA HAIHU

0
984

Daga USMAN NASIDI

YIN abin alkairi ga mutane da ba za su taba mantawa da kaiba, to bawai yana nufin ka baiwa mutum kyautar kudi ba ne kadai, a’a akwai abubuwan da za ka yi wa mutane wanda ya fi karfin ka ba su kyautar kudi, kuma ya sanya mutum ba zai taba mantawa da kai ba.
A kwanakin baya a jahar Legas, wani direban BRT wanda ake ce wa Agape Enyare, aka bayyana cewar ya taimaki wata mai ciki ta haifi jaririyarta mace.
Matar mai ciki dai an bayyana cewar tana neman mota za ta je mile 2, a daidai lokacin sai nakuda ya kamata, a inda nan da nan direban ya durkusa ya taimaka mata ta haifi yarinyar tata, inda ta ji dadi sosai.
An kuma bayyana cewar mamar direban tana aikin amsar haihuwa ne, saboda haka haihuwa ba wai wani abu ne mai tada hankali a wajensa ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here