WANI MUTUM YA YI WA \’YARSA CIKI A KADUNA

0
1310

Daga Usman Nasidi

WANI mutum mai shekaru 40 a duniya, Hafizu Ishaku da ke Kabalan Doki, a karamar hukumar
Kaduna ta Arewa ya yi wa \’yar cikinsa mai shekaru 13 ciki don neman yin asiri.
Matar Ishaku wacce aka kira da suna Maryam ta bayyana wa kotu cewan Hafizu ya yi wa \’yarsu ciki yayin da ta yi tafiya ganin iyayenta na watanni uku.
Ta ce: “Lokacin da na dawo daga ganin iyayena, na lura da canji dangane da \’yata a matsayina na uwa, ba ta da kuzari kamar da a lokaci guda kuma tana rashin lafiya.
Amma ban yi zargin komai ba da farko saboda mijina yana ba ta wasu hade-hade ta sha a kodayaushe wanda yake ikirarin cewa shi zai magance ciwon da ke damun \’yarmu.”
“Amma ciwon ya ki ci ya ki cinyewa kuma na lura cewa \’yata ta yi batan wata, na tilasta mata sai ta fada mun, ta ce mun mahaifinta ne ya yi mata ciki a lokacin da na yi tafiya.
Don haka lokacin da na tunkari Hafizu, ya yi kuka ya fadi gaskiyar cewa ya shiga kungiyar asiri wanda suka tilasta shi ya yi wa \’yarsa ciki ya kuma zubar da shi a matsayin hadaya.”
Ta kara da cewa “Amma bayan an zubar da cikin sai na lura da cewa mahaifin nata ya ci gaba da jima\’i da \’yar tasu.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa ba a samu jin ta bakin Hafizu wanda ke siyar da kayan wuta a kasuwar Maraba Abuja ba a lokacin da ake hada wannan rahoto,amma da zarar an gana da shi za a ji nasa bahasin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here