Za A Sayar Da Wasu Daga Jiragen Shugaban Kasa

0
981

 

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATI ta tallata jirage biyu da ke cikin rukunin jirage goma na fadar shugaban kasa.
Gwamnatin ta yi bayani dalla-dalla a wata sanarwa da aka buga a wasu jaridun kan yanayin jiragen da hotunan ciki da wajensu da kuma ingancinsu.
Sanarwar ta ce ana so a siyar da jiragen biyu kirar Falcon 7X da kuma Hwker 4000 da zarar an samu mai saye.
Kowanne daga cikin jiragen mutune tara yake dauka.
Tun ba yau ba ne \’yan Najeriya da dama suke cewa, kukan karancin kudi da gwamnati ke yi an bar jaki ne ana dukan taiki, saboda yawan jiragen da ke fadar shugaban kasa da kuma makuden kudaden da ake kashewa wajen kula da su.
Wadannan jirage dai biyu ne daga cikin goma da suke cikin jerin jiragen da ke fadar shugaban Najeriya.
Cikin watan Satumba ne dai mai bai wa shugaban Najeriyar shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana da shirin rage yawan jiragen da ke fadar shugaban kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here