Buhari Ya Nada Sababbin Alkalan Kotun Koli Su Biyu

0
1041

\"2016_10largeimg11_oct_2016_143829008\"

Zubair A Sada, Daga Kaduna

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawan Najeriya da su hanzarta tabbatar da mutane biyu a matsayin Alkalan Kotun Koli ta Najeriya.

Shugaban majalisar dattawan, Sanata Bukola Saraki ya karanta wasikar bukatuwar hakan ta shugaban kasa ga \’yan majalisar dattawan a yayin zamansu na majalisar a zauren majalisar yau din nan Talata.

Mutanen biyu da aka zabo domin su zama Alkalan su ne, Sidi Bage daga Jihar Nasarawa da Paul Jauro daga Jihar Taraba.

A wasikar ta shugaban kasa, shugaba Buhari ya ce, neman wannan bukatar da ya yi na bida ka\’idar dokar kundin tsarin mulkin Najeriya a sashe na 231, karamin sashe na 2 cikin baka, wato 231(2) na kwansitushan na Najeriya.

A wata sabuwa kuma, \’ya\’yan majalisar dattawan sun ki amincewa da batun su gurfanar da Daraktan hukumar tsaro na farin kaya (SSS), Lawal Daura a gabanta kan hawan kawarar da wani dan majalisa ya ce ya yi wa Alkalan nan da ake tuhuma.

\’Yan majalisar sun yi watsi da kudurin da Joshua Lidani na jam\’iyyar PDP mai wakiltar Gombe ya kawo gabansu yana neman da a duba wannan cin kashin na cafke Alkalan su 7 da aka yi ranar Asabar da ta wuce.

\’Yan majalisar da farko sun ce, \’ee\’, daga baya suka ce, \’a\’a\’, Sanata Saraki ya yanke cewa, \’yan \’a\’a\’ su ne suka rinjaya, domin haka ba za a gayyato Lawal Daura ba.

Tun farko shugaban marasa rinjaye na majalisar, Godswill Akpabio ya goyi bayan kudurin na a gayyato Lawal Daura gaban \’ya\’yan majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here