TA SHEKA WA WATA MATA RUWAN ZAFI A KAN KAWO GULMAR MIJINTA

0
998

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR ‘Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da wata matar aure mai suna Hassana Rabi’u a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo kan zarginta da sheka wa wata makwabciyarta ruwan zafi don huce haushin tsegunta mata labarin mijinta yana neman wata budurwa a unguwar.
Takardar karar ta bayyana cewa Hassana Rabi’u ta sheka wa makwabciyarta mai suna Hassana Salihu tafasasshen ruwan ne a daidai lokacin da ake kokarin tabbatar da gaskiyar labarin da makwabciyarta ta gaya mata cewa mjinta mai suna Malam Rabi’u yana sumbatar budurwa a wani zaure.
A cewar takardar karar “Lokacin da mijin Hassana Rabi’u ya dawo gida sai ta tunkare shi da wannan tsegumi da makwabciyarta ta gaya mata, wanda a nan take ne mijin nata ya kira mijin makwabciyar a waya, lamarin da ya sa suka hadu a wuri guda don kure mai karya, wanda a wanann lokacin ne ita ma budurwar ta tabbatar da cewa Malam Rabi’un ya kebe da ita.
A daidai wannan lokaci ne ita kuma wacce ake zargin Hassana Rabi’u da takaici ya kama ta sai ta dauko wani ruwa da ke tafasa a kan wuta ta sheka wa Hassana Salihu a kirji lamarin da ya janyo kirjinta ya sabule.”
Alkalin Kotun Mai shari’a Halhalatul-Huza’i Zakariyya ya bayar da umarnin sakaya wacce ake zargin a gidan maza tare da dage shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here