AN KASHE FULANI MAKIYAYA 14 A KADUNA

0
1038

Daga USMAN NASIDI

WASU gungun matasa sun hallaka \’yan Fulani makiyaya su 14 har lahira tare da kone su kurmus a karamar
hukumar Jema’a da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a tsakanin ranakun hutun karshen mako zuwa Litinin kuma ya afku ne sakamakon dadadden rigima da ke tsakanin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya.
Wani shedan gani da ido, kuma direba ya bayyana cewa matasan sun fitar da yan Fulani su 8 daga motarsa inda suka sassara su, yayi da ya tafi neman bakanike da zai gyara mai motarsa data mutu a kan hanya.
Ya ce “Ina hanyar dawowa daga Filato ne inda na dauko fasinjoji 8, dukkaninsu yan Fulani, yayin da na tafi neman kanikawa ne matasa suka kashe su” inji direba Adamu Aliyu.
Direban ya cigaba da cewa “bayan sun kashe su, sai suka mayar da gawarwakinsu a cikin motar, inda suka
banka mata wuta, haka suka yi ma wata mota da ta tsaya shan mai, inda suka kashe duk mutanen cikin motar, su shidda.
Daga nan ne sai Sojoji da \’yan sanda suka bazama a kan hanyar suna kame, ni kuma sai na dawo wajen motata, amma na tarar da ita a kone tare da birbishin gawawwakin fasinjoji na”.
Shi ma shugaban karamar hukumar Jema’a Bege Katuka ya tabbatar da faruwar hatsaniya a yankin nasa inda ya ce “A ranar Asabar ne wasu da ake zargin Fulani ne suka kai hari garin Godogodo inda suka bude wuta aka jama’a.
Sai washegari kuma matasan garin suka tare babbar hanya suna farfasa motocin tare da kashe mutane masu bin hanyar.” Inji Katuka.
Kakakin rundunar \’yan sandan Jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace mutane biyu kacal aka kashe.
A wani labarin kuma an bindige wasu \’yan sanda su uku a ranar Litinin 17 ga watan Oktoba a garin Hawan Kibo
da ke kan iyakar jihar Kaduna da Filato, duk da cewa ba mu samu jin ta bakin Kaakin rundunar ta Jihar Filato ba, wata majiya daga rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace an tafi da makaman \’yan sandan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here