An Sace Wani Babban Malami A Sakkwato

0
942

 

Rabo Haladu Daga  Kaduna

WADANSU barayin mutane sun afka gidan wani fitaccen malami a Jihar Sakkwato inda suka yi awon gaba da shi.
An sace Malam Muhammad Lawal Maidoki, shugaban hukumar raba Zakka ta jihar ne, jiya Laraba a hanyar Abuja.
Tun da fari dai rahotanni na cewa barayin sun sace malamin ne tare da matarsa da \’ya\’yansa.
Duk yunkurin da aka yi domin kai wa ga barayin ya ci tura.
Sai dai wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa barayin sun bukaci a biya su wasu kudade kafin su sake shi.
Najeriya dai ta yi kaurin-suna wajen yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, inda ko a baya-bayan nan sai da barayin mutanen suka sace matar shugaban babban bankin kasa  Godwin Emefiele.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here