WASU MATASA SUN BANKA WA OFISHIN \’YAN SANDA WUTA A ZAMFARA

0
979

Daga Usman Nasidi

WASU matasa sun banka wa ofishin \’yan sandan kauyen Magazu da ke karamar hukumar Tsafe wuta bayan samun sabani tsakanin jama’an kauyen da \’yan sandan.
Wani sheda na gani da ido da ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wa manema labarai cewa sabanin ya samo asali ne bayan wani mai laifi Ibrahim Muhammad da ke kulle a ofishin \’yan sandan ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Ibrahim ne sakamakon sace na’urar wayar tarho ne da ya yi.
A cewar majiyar, mutuwar Ibrahim ne ya harzuka matasan yankin, inda suka tasar wa ofishin \’yan sanda suka farfasa shi tare da banka masa wuta.
Shi ma Kakakin rundunar \’yan sanda na jihar Shehu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin. Kaakakin ya ce tuni hukumar tasu ta fara tattara bayanin rahoton yadda lamarin ya kasance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here