Shugaban Hukumar Filayen Jiragen Saman Nijeriya Ya Zama Shugaban Kungiyar Filayen Jiragen Saman Afrika

0
817

Isah Ahmed, Jos

AN zabi Janar Manajan hukumar filayen jiragen sama ta Nijeriya [FAAN] Injiniya Saleh Dunuma a matsayin sabon shugaban kungiyar filayen jiragen sama ta Afrika (ACI). An zabi Injiniya Saleh Dunuma  a matsayin sabon shugaban  kungiyar ta filayen jiragen sama ta Afrika ne a taron da kungiyar ta gudanar a Maputo, babban birnin kasar Mozambique.
Kuma an zabi Ijiniya Saleh Dunuma a matsayin sabon shugaban kungiyar ne bayan da wa\’adin tsohon shugaban kungiyar, Mista Pascal Komla wanda ya fito daga kasar Togo ya cika. Injiniya Saleh Dunuma shi ne dan Nijeriya na farko da ya fara rike shugabancin kungiyar tun daga lokacin da aka kafa ta.
Shi dai Injiniya Saleh Dunuma ya fara aiki da hukumar filayen jiragen Sama ta Nijeriya [FAAN] ne tun a shekarar  1980, a inda ya rike mukamai daban-daban a hukumar, har ya zuwa mukamin Janar Manajan hukumar da yake kai a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here