Kwamishiniyar ‘Yan Sanda Ta Zama Shugabar Kwalejin Oxford

0
1004

 

Zubair A Sada, Daga Kaduna

MATAIMAKIYAR kwamishiniyar ‘yan sanda (AC) Helen King ta bayyana ajiye ritayarta daga aikinta na ‘yar sanda na tsakiyar birnin London, kuma ta kasance mace ta farko da aka zaba ta zama shugabar makarantar kwalejin St Anne da ke jami’ar Oxford, a inda za ta fara aikinta a cikin watan Afrilun shekarar 2017.

Helen King ta ce, ‘’Ina mai alfahari da zamana jami’ar ‘yar sanda na fiye da shekaru 30, kuma ina kara yin alfahari babba na kasancewata mamba ta ‘’Met’’ a matsayin jami’a babba da ke kula da harkokin ‘yan sanda a wannan yankin da kuma kwarewa’’.

Ta ce dukkan wadannan alfahari sun biyo bayan abin da ta gani ne daga abokanan aikinta suna cimma nasarorinsu a birnin na London tun daga sassanyar safiya zuwa wata sassanyar safiyar, wato awoyi 24 kowace rana a ranakun shekara. Abokanan aikin nata kamar yadda ta ce, suna aikinsu ne da ilimi da zimmar aikin da mutunci da kyautatawa da suke gabatarwa a lokuta masu yanayi na wahalhalu sosan-sosai.

Daga karshe Helen King ta ce za ta yi iyakacin kokarinta na ciyar da kwalejin gaba, domin ta san kwalejin ciki da wajenta, domin kuwa a nan ne ta yi digirinta na farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here