Ana Ta Hako Manya-Manyan Tukwanen Kasa A Kano

0
1184

Rabo Haladu Daga  Kaduna

AN hako wasu manyan tukwanen kasa a unguwar Zangon Bare-bari a karamar hukumar Nassarawa da ke tsakiyar birnin Kano.
Masu hasashe dai na cewa tukwanen ka iya kai wa shekaru 500 a duniya, ko da yake gwajin kimiyya ne kadai zai iya tabbatar da haka.
Tun bayan gano tukwanen ne a wani gida da ake sabunta ginawa, wasu da ba a san ko su wane ne ba suka haura da tsakar dare suka fasa daya daga cikin tukwanen da nufin kwashe abin da ke ciki.
Mai unguwar Zangon Barebari Malam Auwalu Rabi\’u inda aka gano tukwanen, ya shaida wa manema labarai cewa tukwanen guda uku da ke cikin wani katon rami, manya-manya ne kamar girman mutum.
Ya ce bayan da aka gano su ne a ranar Alhamis aka shaida masa, inda shi kuma ya sanar da hukuma.
A makonnin baya ma, an gano irin wadannan tukwane a yankin Rangaza a karamar hukumar Nassarawa a birnin na Kano.
A shekara biyar zuwa shida da suka gabata ma a unguwar Agadasawa da ke birnin Kanon an taba samun tukunya daya , amma ba ta kai girman wadannan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here