ANA SA RAN SHUGABA BUHARI ZAI KARA ALBASHIN MA\’AIKATA

0
1040

Daga Usman Nasidi

ANA san ran shugaba Buhari zai kara albashi na ma’aikata bayan ya gana da kungiyar kwadago ta kasa wato NLC.
Shugaban wani bangare na NLC din ya tabbatar da cewa kungiyar za ta gana da shugaba Buhari domin tattaunawa game da batun.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa wato NLC, Ayuba Wabba ya bayyana cewa NLC za ta zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da kungiyar kwadago ta kasa NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya wato TUC.
Ayuba Wabba, shugaban wani bangare na kungiyar NLC ya ce sun gabatar da rokon su ga shugaba Buhari, ana kuma sa ran ya duba wannan batu. Jaridar Daily Times ta rahoto cewa kungiyar kwadago na kokarin ganin an maida albashin ma’aikata ya kai akalla N56000 a kowane wata.
kungiyar kwadago ta kasa da kuma kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya wato TUC sun gana a tsakanin su a ranar Litinin, kafin su je su samu shugaba Buhari domin fara zama.
A yanzu dai mafi karancin albashin ma’aikatan tarayya a kasar shi ne N18000, wanda tun lokacin shugaba Jonathan aka sama hannu.
Ana neman shugaba Buhari ya kara albashin ma’aikata zuwa akalla N56000 a kowane wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here