ANA TSARE \’YAN SANDA 17 A KAN LAIFIN CIN HANCI

0
1090

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR \’yan sandan jihar Legas tace tana tsare da jami’anta su 17 da ta kama kan zargin aikata laifuka irin na rashin da’a daban-daban, ciki har da karbar na goro.
Rahotannni sun bayyana cewa \’yan sandan sun shiga hannu ne a tsakanin ranakun 6 ga watan Oktoba da 28 na watan, kuma a yanzu haka ana kan binciken su kamar yadda dokokin hukumar ta tanadar.
Rahoton ya jiyo wata majiya tana fadin cewa wasu daga cikin yansandan ka iya rasa aikinsu, yayin da wasu kuma za’a rage musu mukami. Kwamishinan \’yan sandan jihar Legas Fatai Owoseni ya tabbatar da kama \’yan sandan, kuma ya tabbatar wa jama’a hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk dan sandan da ta kama yana saba dokokin ta.
Ya ce “kimanin \’yan sanda 17 ke tsare a hannun hukumar \’yan sanda, an kama \’yan sandan a unguwanni daban- daban na jihar. Kuma muna nan muna duba irin horon da za a musu wanda ya yi daidai da laifukansu. Rundunar \’yan sanda na yin kan- jiki kan-karfi wajen gudanar da ayyukanta yadda ya dace.
Kwamishinan ya ci gaba da fadin “ba za mu laminci miyagun laifuka ba. Bugu da kari mun kama yan fashi da makami su 26, da masu garkuwa da mutane su 18. Sa’annan mun kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu, bindigar toka 14 da harsasai 193 daga hannayensu.
Kwamishinan \’yan sanda Owoseni ya karkare da fadin “a samamen da muka kai yankuna daban-daban, mun samu nasarar kwato motoci 17 da wayoyi 11 a hannun miyagun mutane.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here