AN YI GARKUWA DA WASU MUTANE 5 A JIHAR EKITI

0
840
Daga Usman Nasidi

AN yi garkuwa da mutane 5 a jihar  Ekiti a ranan Asabar, 5 ga watan Nuwamba 2016 inji Gwamna Ayo Fayose.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka yi garkuwa da su su ne Fasto Ojo da direbansa da kuma wasu guda 3.
Mutanen sun kasance suna bulaguro ne zuwa karamar hukumar Ise/Orun ta jihar inda hakan ya faru.
Kakakin jami’an \’yan sandan jihar, wanda ya tabbatar da faruwar al\’amarin ya ce an saki mutane 2 daga cikinsu.
Ya ce jami’an \’yan sanda na kan hanyar ceto sauran guda 3 da aka yi garkuwa da su kuma ya yi kira da mutanen unguwan su taimaka wa \’yan sanda wajen samun maboyar su.
Wannan na faruwa ne kwana daya kacal bayan da aka yi garkuwa da sakataren hukumar gudanar da zaben jihar Ekiti, Barrista Muslim Olujide Omoleke.
An yi garkuwa da Barrister Muslim Olujide Omoleke ne da yaronsa da kuma direba a titin Ilesha/Akure a ranar juma’ar nan da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here