Ba Son Kai A Yaki Da Cin Hanci\’

0
870

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATI  ta musanta zarge-zargen cewa tana nuna son kai da siyasa a yaki da cin hanci da rashawa.
Ministan shari\’a na Najeriya, Barrister Abubakar Malami ya shaida wa manema labarai cewa duk wanda aka samu da laifin wawure kudin gwamnati za a gurfanar da shi gaban kuliya.
Ya kara da cewa babu wata doka da gwamnatin kasa ke karyawa wajen tsarewa da kuma gurfanar da wadanda aka samu da laifin almundahana da cin hanci da rashawa.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati a Najeriyar dai na binciken jami\’ai da dama, kuma galibinsu na tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa ana musu bi-ta-da-kulli ne irin na siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here