AKALLA MUTANE 7 SUKA RASA RAYUKANSU A WANI HADARIN KWALE-KWALE

0
815
Daga Usman Nasidi

AKALLA mutane 7 ne suka rasa rayukan su a wani hadarin jirgin kwale-kwale da ya faru a rafin Gbako a karamar hukumar Katcha a Jihar Neja.
Hadarin kwale-kwalen ya zama ruwan dare a Najeriya musamman cikin karkara, abin takaicin shi ne, mutane 3 \’yan dangi daya sun rasa rayukansu a hadarin.
Malam Ahmed Inga, Dirakta Janar na hukumar bayar da taimako na gaggawa ,shiyar Jihar Neja, ya fada wa manema labarai a Minna cewa mata 4 da yara 3 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar nutsewa da suka yi.
Ya kara da cewa kwale-kwalen ya dauki mata 10 manoma daga Unguwan Balsa zuwa wata gonar shinkafa bayan an tsallake rafin.
Malam Ahmed Inga, ya ce an ceto rayuwar mata 3 a hadarin wanda ya faru misalin karfe 11 na safe.  “Yabagi Ibrahim,mai gonar ya rasa matarsa da ‘yar sa, da jikarsa a hadarin.
” Ya ce watanni biyu da suka gabata, wani mai yi wa kasa hidima, mai suna Dayo,ya rasa ransa sanadiyyar fada wa cikin rafi daga cikin kwale-kwale a Jihar Kuros-Riba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here