An Kashe \’Yan Kunar-Bakin-Wake A Maiduguri

0
898

Rabo Haladu Daga  Kaduna

RAHOTANNI daga birnin Maiduguri na jihar Borno na cewa an kashe wasu \’yan kunar-bakin-wake da suka yi yunkuri tayar da bama-bamai da safiyar Juma\’a.
Jamian tsaro suna cewa maharan uku, wadanda dukkan su mata ne, sun yi yunkurin shiga birnin Maiduguri ne amma an ci lagonsu aunguwar Ummurari da ke wajen birnin.
Kungiyar Boko Haram ce dai ke kai hare-hare a birnin da ma wasu yankuna na jihar ta Borno da makwabtan jihohi.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar, kuma nan ba da dadewa ba za ta kawar da ita daga doron kasa.
Ko a makon jiya sai da mayakan kungiyar suka kashe wasu sojin Najeriya, cikin su har da Latftanar Kanar Muhammad Abu Ali, wani soja da ya yi suna wajen ragargazar mayakan Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here