BA NI NA KASHE KUDIRAT ABIOLA BA – Inji Manjo Almustapha

0
1267

Daga Usman Nasidi

TSOHON mai tsaron shugaban kasa Manjo Hamza Al-Mustapha ya musunta zargin da ake masa na kisan Kudirat Abiola kuma ya musanta hannunshi aikin abubuwan da suka tattari mutuwarta.

Major Hamza Al-Mustapha wanda ya kasance mai tsaron marigayi Janar Sani Abacha ya bayyana ana jingina shi da kisan uwargidan Abiola, wanda ya lashe zaben shekarar 1993 amma Babangida ya danne.

A wani jawabin darya gabatar a wajen  lakcan Dakta Fredrick Fasehun a Akure a ranan Laraba,9 ga watan Nuwamba inda ya wanke kansa daga kisanta.

Ya ce “Ana bata mini suna, na yi aikina ne yadda ya kamata na tsare shugaban kasa, kare gwamnati da mutanen kasa.”

Ya yi kira ga \’yan Najeriya su hada kai domin kawo ci gaban Najeriya duk da banbance-banbancen siyasa.

Ya ce “Akwai taratsi da yawa, rowa, da son kai. Muna ci baya ne kullum. Damuwa ta shi ne a so kasar nan kuma a taimaka wa ci gaban ma’aikatu ba lalata su ba, abin da ya kamata mu lura da shi kenan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here