Farashin Kayan Masarufi Na Kara Hauhawa

0
961

Rabo Haladu Daga  Kaduna

HUKUMAR kididdiga ta kasa ta ce farashin kaya a Najeriya ya karu da kusan sama da kashi 18 bisa dari a cikin watan Nuwamba.
Ta ce farashin kayan ya yi tashin gwauron zabin da bai taba yi ba a cikin shekaru 11, wanda hakan wata alama ce ta karin matsin tattalin arziki a kasa.
Farashin da ya fi tashi shi ne na gidaje, da ruwan sha, da wutar lantarki, da na gas, da sauran makamashi, in ji hukumar.
Shi ma farashin kayan abinci ya tashi zuwa sama da kashi 17 cikin dari a watan Oktoba, idan aka kwatanta da kashi 16 da rabi a watan Satumba.
Najeriyar wacce mamba ce a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, kuma mafi girman arziki a Afirka, na fuskantar matsin tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 25.
Faduwar farashin mai da yawan kai hare-hare kan bututun man a yankin Neja-Delta na haifar da koma baya na danyen man da kasar ke hakowa.
Ya kuma haddasa karancin Dalar Amurka, da hakan ya yi mummunan tasiri kan harkokin kasuwancin shigowa da kayayyakin ciyar da masana\’antu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here