Majalisa Ta Yi Watsi Da Sunayen Jakadun Da Buhari Ya Aika Mata

0
821

Rabo Haladu Daga  Kaduna

MAJALISAR dattawan ta kada kuri\’ar kin amincewa da sunayen jakadu 46 da shugaba Buhari ya aike mata don tantancewa.
\’Yan majalisar sun ce za a sake mayar wa da shugaba Muhammadu Buhari sunayen \” domin ya yi musu garanbawul\’\’
Shugaban masu rinjaye na majalisar Ali Ndume ne ya gabatar da bukatar mayar da sunayen ga shugaba Buharin, yayin da shugaban marassa rinjaye, Godswill Akpabio na PDP ya mara masa baya.
Sun ce sun samu koke-koke da dama kan tsarin da aka bi wajen zabo sunayen wadanda za a bai wa mukamin jakadun Najeriyar a kasashen waje.
Wasu daga cikin sanannun da sunayensu ke ciki akwai tsohon alkalin kotun kolin kasar Justice George Oguntade; da Yusuf Tugar daga jihar Bauchi, da Mohammed Hayatuddeen daga Jihar Borno, da Jamila Ahmadu-Suka daga jihar Sokoto.
Gwamnonin jihohi sun nuna rashin jin dadinsu kan rashin tuntubar su da shugaba Buharin ya yi cikin wadanda za su zabi Jakadun, inda suka ce mutanen ba \’yan siyasa ba ne.
A ranar 20 ga watan Oktoba ne Buharin ya aike wa da majalisar dattawan wasikar neman amincewa da sunayen mutanen 46 da suka hada da Olorunmimbe Mamora da Dakta Usman Bugaje, wanda ya ki karbar tayin mukamin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here