An Sace Mutane Fiye Da 40 A Zamfara

0
939

Rabo Haladu Daga  Kaduna

RAHOTANNI daga Jihar Zamfara   sun ce \’yan bindiga masu fashin shanu sun sace mutane fiye da arba\’in a jihar.
A ranar Juma\’a ne da dai masu fashin shanun suka sace mutanen a lokaci guda domin yin garkuwa da su.
Akasarin mutanen da suka yi awon gaba da su dai \’yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa daga kauyukansu.
Rahotannin sun kara cewa \’yan sanda biyu da fararen hula hudu sun rasa rayukansu a cikin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here